Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Wata majiya ta soji mai girma ta shaida cewa sojojin Iran za su mayar da martani ga cin zarafin daren yau na Amurkawa bayan kai hari ga wasu wurare na kasar, kuma wannan martani zai ninka yawan hare-harensu.
Ta jaddada cewa: "Kamar yadda muka yi gargaɗi a baya kuma muka yi alkawari, sojojin Iran za su nuna martani mai tsanani da fa'ida ga duk wani hari a kan ƙasa da muradun kasar."
Wannan majiya ta soji ta sanar da cewa: "Muradun da sansanonin Amurka a yankin za su shiga cikin hare-haren Iran ba da daɗewa ba."
Ta kuma ce a karshe: "nade tabarmar hauka sakamakon gazawa, ta jefa Amurkawa cikin rudani da mamaki; wannan ya sa duk lokacin da suka yi wauta, suna kara kunyata kansu ne.
………………………..
Ra'ayinka